Dan gwagwarmayar kare hakkin dan’Adam kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, ya mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka, Donald Trump da ya bayyana cewa Kiristoci na fuskantar barazana a Nijeriya.
A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, Sowore ya ce ceto Nijeriya ba zai fito daga waje ba, sai dai daga ingantaccen shugabanci a cikin gida. Sannan matsalar Nijeriya ba ta takaita ga addini ba, illa sakacin gwamnati, cin hanci, da rashin shugabanci mai nagarta.
Jaridar Punch ta ruwaito Sowore ya kara da cewa duka Kiristoci da Musulmai na fama da hare-haren ‘yan bindiga da talauci a sassa daban-daban na kasar, maimakon a rika kallon matsalolin tsaro ta fuskar addini, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su hada kai wajen neman shugabanci nagari da kare rayukan jama’a.



