Wasu jam’iyyun adawa a Nijeriya na zargin Shugaba Bola Tinubu da amfani da kudaden gwamnati da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa domin tilasta wa ‘yan adawa su koma jam’iyyar APC.
A cewar kakakin jam’iyyun PDP, NNPP da CUPP, wato Debo Ologunagba, Oladipo Johnson, da Mark Adebayo, sauya shekar da ake ta gani daga ‘yan adawa zuwa APC na nuna cewa jam’iyyar mai mulki na dab da rugujewa daga ciki.
Sai dai kakakin yaɗa labarai na APC, Bala Ibrahim, ya karyata zargin, yana mai cewa wadanda suka koma jam’iyyar sun yi hakan ne da son ransu saboda irin nasarorin da APC ke samu a mulki, kuma jam’iyyar na da cikakken tsari da zai hana ta fadawa rikicin cikin gida.



