Wani lauya kuma tsohon mai ba da shawara ga shugaban kasa, Chief Okoi Obono-Obla, ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da wasu bangarorin gwamnatin Amurka da yin nuni da karya da kuma raini kan zargin cewa ana kisan Kiristoci a Nijeriya.
Yayin da yake magana a Calabar a ranar Lahadi, Obono-Obla ya bayyana matakin Amurka a matsayin diplomasiyya mai cike da ruɗani wadda ke nuna girman kai da son nuna karfi, yana mai cewa Amurka na amfani da batun addini ne domin kawo rudani a Nijeriya.
Okoi ya kara da cewa, ita kanta Amurka na fama da hare-haren ‘yan bindiga a majami’u amma ba ta bukaci sojojin kasashen waje su shigo mata ba, to bai kamata ta tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Nijeriya ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, lauyan ya gargadi Amurka da cewa duk wani yunƙuri na kutse a cikin harkokin Nijeriya da sunan kare addini zai zama karya doka a matakin kasa da kasa.



