Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya musanta wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ya yi izgilanci ga shugaban Amurka Donald Trump kan barazanar yaƙi da Nijeriya.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Eseme Eyiboh, ya fitar a Abuja ranar Litinin, Akpabio ya ce kalaman da aka danganta masa ƙarya ce kuma ƙoƙari ne na tayar da husuma tsakanin shi da shugaban Amurka.
A cewarsa, rubutun da wata kafar sada zumunta mai suna Rant HQ ta wallafa ba gaskiya ba ne, tare da zargin masu yada shi da neman haddasa rikici tsakanin Nijeriya da Amurka.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, sanarwar ta ƙara da cewa hoton da aka haɗa da rubutun an yi amfani da shi ne wajen ƙara wa ƙaryar armashi, domin ya sa jama’a su gaskata abin da bai furtawa ba.



