Shugabar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta karbi rantsuwa a ranar Litinin bayan zaben da aka yi cikin tashin hankali kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Jam’iyyar adawa ta Chadema ta ce daruruwan mutane sun rasa rayukansu a hannun jami’an tsaro amma hukumar zabe ta bayyana cewa Suluhu ta lashe zaben da kashi 98 cikin dari.
An gudanar da bikin rantsuwar a fadar gwamnati da ke Dodoma ba tare da halartar jama’a ba, yayin da intanet ke a katse gaba ɗaya tun ranar zabe, wanda hakan ya hana samun sahihan bayanai daga kasar.
Wata majiyar diflomasiyya ta ce an samu rahotannin mutuwar mutane da dama a asibitoci, yayin da Chadema ta bayyana cewa sama da mutum 800 ne suka rasa rayukansu, duk da cewa babu tabbacin wannan adadi.
Hukumomin kasar sun musanta zargin amfani da karfin iko, yayin da makarantu da sufuri suka tsaya cak a fadin kasar kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.


                                    
