Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta fitar da sanarwa mai dauke da watsi kan zargin cewa hare-haren ta’addanci da ke ƙaruwa a yankin suna da alaka da halaka wasu mabiya addini, tana mai jaddada cewa ta’addanci yana shafar kowa ba tare da bambancin addini ko kabila ba.
A sanarwar da ta fitar a ranar Talata, ECOWAS ta bayyana cewa kungiyoyin ta’addanci na kai hare-hare a kasashe da dama ciki har da Nijeriya, inda ake hallaka fararen hula ba tare da bambanci ba.
Kungiyar ta yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙasashe abokan hulɗa da su cigaba da tallafa wa kasashen yankin wajen yaki da tsattsauran ra’ayi da ta’addanci.
Sanarwar ta zo ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana Nijeriya a matsayin “ƙasa mai damuwa ta musamman,” bisa zargin cewa ana barazana ga Kiristoci, abin da gwamnatin Nijeriyar ta musanta.



