Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya gabatar da kasafin kudin jihar na shekarar 2026 wanda ya kai Naira biliyan 897.8 a zauren majalisar dokokin jihar, inda ya ce sabon kasafin ya fi na bara da kaso 29.7 cikin dari.
Radda ya ce kashi 81 cikin 100 na kudaden za a kashe su ne wajen manyan ayyukan ci-gaba, yayin da kashi 18.6 cikin 100 zai tafi wajen biyan albashi da sauran kudaden gudanarwa, kuma kasafin zai mayar da hankali kan fannin ilimi, lafiya, noma da samar da ruwa.
A cewar gwamnan, ma’aikatar ilimi ce ta samu kaso mafi tsoka da fiye da naira biliyan 156 domin bunkasa ingancin karatu da gina sabbin makarantu a fadin jihar wanda hakan na cikin kokarin gwamnatinsa na gina tushe mai karfi ga ci-gaban jihar.
Hakazalika, Radda ya ce za a cigaba da aiwatar da kasafin ta hanyar sauraron bukatun al’umma daga kananan hukumomi da kauyuka, tare da tabbatar da tsaro da farfado da tattalin arzikin karkara.



