Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bar Abuja zuwa Brazil domin wakiltar shugaba Bola Tinubu a babban taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya karo na 30 da za a gudanar a birnin Belém na kasar Brazil.
Taron, wanda shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva ke jagoranta tare da hadin guiwar wasu kasashe, zai gudana daga ranar 6 zuwa 7 ga watan Nuwamba, inda za a tattauna batutuwan da suka shafi kariyar dazuka, halittu, da adalcin yanayi.
Mai magana da yawun ofishin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha, ya bayyana cewa Shettima zai gabatar da jawabin Nijeriya kan sauyin yanayi, sannan ya halarci tarukan kwamitoci da za su tattauna batun canjin makamashi da yarjejeniyar Paris.
Haka kuma, Shettima zai yi ganawa da shugabanni da masu ruwa da tsaki don tattauna yadda Nijeriya za ta shiga kasuwar carbon finance da ake sa ran za ta samar da har dala biliyan uku a duk shekara.



