Majalisar dattawan Nijeriya ta bayyana cewa za ta gana da shugaba Tinubu da bangaren zartarwa domin tattauna batun rikicin diflomasiyya da kalaman shugaban Amurka Donald Trump kan zargin kisan Kiristoci a kasar.
Trump ya yi wannan furuci ne bayan da Amurka ta sanya Nijeriya cikin jerin “kasashen da ke da damuwa ta musamman” saboda zargin wariyar addini, lamarin da ya jawo musayar yawu a tsakanin jakadun kasashen biyu.
Da yake jawabi a zauren majalisar a ranar Talata, shugaban majalisar dattawan Godswill Akpabio ya ce batun na da nasaba da manufofin diflomasiyya, don haka sai sun tuntubi gwamnatin tarayya kafin su dauki matsaya, sannan kuma kalaman Trump sun dogara ne da “tsohon rahoto na shekarar 2010” wanda bai yi daidai da halin da ake ciki a yanzu ba.
A cewarsa, matsalar tsaro a Nijeriya ba ta da alaka da addini, inda ya ce Musulmai da Kiristoci duka na fuskantar hare-hare iri daya daga ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga.



