Shugaba Bola Tinubu ya aika wa majalisar dattawan Nijeriya wasikar neman tantancewa da tabbatar da Dr. Kingsley Tochukwu Ude, babban lauya daga Jihar Enugu, a matsayin sabon minista.
Shugaban majalisar dattawan, Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar a zaman da aka gudanar ranar Talata, inda ya mika sunan Ude ga kwamitin tantancewa don ci-gaba da nazari.
Nadin ya biyo bayan murabus din tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, wanda ya ajiye aiki saboda rikicin takardun karatu da na yi wa kasa hidima wato NYSC.
Dr. Ude, wanda ke rike da mukamin kwamishinan shari’a na jihar Enugu, zai maye gurbin Nnaji a majalisar zartarwa ta Tinubu.



