Kungiyar dattawan Arewa ta jam’iyyar PDP ta zargi ministan tsaron Nijeriya, Bello Matawalle, da jagorantar sauya shekar da dama daga PDP zuwa APC ta hanyar abin da ta kira cin hanci da tsoratarwa.
A wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na kasa, Dr Abbas Sadauki, ya fitar, ta ce, tsohon gwamnan na Zamfara yana amfani da mukaminsa da dukiyar da ya mallaka wajen jan magoya bayan PDP musamman a jihohin Zamfara da Kaduna su koma jam’iyyar APC.
Ƙungiyar ta ce matakin Matawalle wani yunkuri ne na raunana jam’iyyar PDP a yankin Arewa maso Yamma kafin zaɓen 2027, tana mai gargadin cewa, amfani da kuɗi da barazana wajen rusa jam’iyyar adawa na haifar da barazana ga dimokuraɗiyya.



