Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya nemi amincewar majalisar dattawa don karbo rancen Naira tiriliyan 1.15 daga kasuwar cikin gida domin cike gibin kasafin kuɗin shekarar 2025.
Wannan buƙata ta kasance cikin wasikar da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta a zauren majalisa yayin zaman da aka gudanar a ranar Talata.
A cikin wasikar, Tinubu ya bayyana cewa rancen ya zama dole don samar da kuɗin da za a yi amfani da su wajen aiwatar da manyan shirye-shiryen gwamnati da ayyukan raya ƙasa.
A cewarsa, wannan tsari na rance wani ɓangare ne na dabarun gwamnati don farfaɗo da tattalin arziƙi, samar da ayyukan yi, da tabbatar da ci-gaban ƙasa.
Majalisar ta tura buƙatar zuwa kwamitin bashi na cikin gida da na ƙasashen waje domin yin nazari da bayar da rahoto cikin mako guda.



