Madugun adawar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, wanda ya kalubalanci nasarar Paul Biya, yana iya kasancewa yana a Nijeriya kamar yadda Africa Intelligence ta ce, amma wasu majiyoyi sun ce ya koma Abuja a ruwaitowar jaridar Daily Trust.
Rahoton ya ce an fitar da shi daga gidansa da ke Marouaré a Garoua tsakanin 28 da 29 ga watan Oktoba inda a sakonsa na Facebook, ya gode wa sojojin da suka raka shi zuwa wuri mai aminci.
A cewar rahoton, an tsallaka da shi zuwa Nijeriya bayan fargabar kai masa hari daga jami’an tsaro yayin da a safiyar 29 ga watan Oktoba, aka ji harbe-harbe a unguwarsa.
Ministan harkokin cikin gida, Paul Atanga Nji, ya gargade shi kan tada rikicin bayan zabe, yana mai cewa ya karya doka da ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zabe kafin sakamakon hukuma ya fita.



