Tsohon mai ba wa shugaban kasa shawara, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya bukaci shugaba Bola Tinubu da ya fito fili ya yi wa ’yan Nijeriya jawabi kan barazanar mamayar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa ƙasar.
A wata sanarwa da ya wallafa a Facebook ranar Alhamis, Baba-Ahmed ya bayyana damuwa cewa shugaban kasa bai ce komai kai tsaye ba tun bayan da lamarin ya faru kuma wannan shiru na iya nuna rauni da rashin tsari a shugabanci.
A cewarsa, bai kamata ministoci ko kakakai su rika magana ba, sai shugaban kasa da kansa ya fito ya tabbatar da matsayin Nijeriya da matakan da gwamnati ke ɗauka.
Haka kuma ya gargadi Tinubu da kada ya yi niyyar tafiya Amurka don ganawa da Trump, yana mai cewa hakan zai kara bata sunan Nijeriya.
Baba-Ahmed ya bukaci shugaban kasa da ya dauki mataki cikin gaggawa ta hanyar nada jakadu, farfaɗo da hulɗar diflomasiyya, da yin jawabi kai tsaye ga ’yan ƙasa don tabbatar da cewa Nijeriya tana da murya da matsayin kanta.



