Babban hafsan sojin saman Nijeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya ce rundunar sojin sama za ta mayar da hankali kan kare rayukan fararen hula da gujewa mummunan hari kan farar hula yayin ayyukanta.
Aneke ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin ganawarsa ta farko da manyan hafsoshin rundunar a hedikwatar rundunar da ke Abuja, inda ya ce wannan mataki na cikin abin da shugaban Bola Tinubu ke bukata daga dakarun kasa.
Aneke ya ce rundunar za ta karfafa hulɗa da al’umma da kuma hadin kai da sauran hukumomin tsaro domin murkushe ta’addanci da hana maƙiya samun mafaka, sannan kuma kare rayukan fararen hula da gujewa mummunan hari shi ne ginshikin kwarewar aikin.
Hakazalika, ya kuma tabbatar wa hafsoshin cewa dukkan matakan rundunar za su bi umarnin shugaban kasa kai tsaye, tare da mayar da hankali kan inganci, tsaro da kare martabar sojin sama.



