Gudunmuwar da sarakunan gargajiya ke badawa wajen samar da zaman lafiya, ba abin yadawa ba ce – Kungiyar International Alert
Ƙungiyar International Alert Nigeria ta bayyana cewa sarakunan gargajiya na taka muhimmiyar rawa wajen hana rikice-rikice a jihohin Zamfara da Katsina.
Shugaban ƙungiyar a Nijeriya, Sunday Momoh Jimoh, ne ya bayyana hakan a jawabin maraba yayin bude taron horar da sarakuna da manyan shugabannin al’umma kan warware rikici da hanyoyin daidaitawa, wanda aka gudanar a Katsina.
Ƙungiyar International Alert, wacce ba ta gwamnati ba ce, tana aiki a Nijeriya don ƙarfafa zaman lafiya, ƙarfafa cibiyoyin al’umma, da bunƙasa tattaunawa tsakanin jama’a.
Mr. Jimoh ya jaddada cewa ba za a iya watsar da rawar da sarakuna ke takawa ba wajen rage tashin hankali da rikice-rikice, inda ya ce horon na da nufin ƙara musu ƙwarewa wajen sasantawa da warware rikici ta hanyar da ta dace kuma mai adalci.
Ya kuma tabbatar da cewa ƙungiyar tana da niyyar ci gaba da tallafa wa gwamnoni da cibiyoyin shari’a domin inganta warware rikici a matakin ƙauyuka da al’umma.
Mahalarta taron sun haɗa da jami’an ma’aikatun Shari’a, Hukumomin Kananan Hukumomi da Masarautu, da kuma sarakunan gargajiya daga jihohin Zamfara da Katsina.



