Wasu ’yan majalisar dokokin Amurka tara sun rubuta wa sakataren harkokin wajen kasar, Marco Rubio, suna nuna damuwa kan tashin hankali, kisa, da kama mutane da dama da suka biyo bayan zaben shugaban kasa na Kamaru da aka gudanar a ranar 12 ga watan Oktoba.
A cikin wasikar, ’yan majalisar sun soki yadda gwamnati ke danniya kan masu zanga-zanga cikin lumana, tare da kira da a hukunta wadanda ke da hannu wajen kashe fararen hula. Sun bukaci gwamnatin Amurka ta matsa wa hukumomin Kamaru lamba domin su mutunta dimokuradiyya da hakkin dan Adam.
Wannan mataki ya biyo bayan yadda ake samun matsin lamba daga kasashen duniya, bayan rahotannin kashe mutane da dama da kama daruruwan mutane da kuma takurawa ’yan adawa bayan sake zaben shugaba Paul Biya da ake tantama a kai.
Masana harkokin diflomasiyya na ganin wannan matakin na ’yan majalisar Amurka a matsayin alamar cewa Washington na bin lamarin Kamaru da ido sosai kamar yadda jaridar MMI News ta wallafa.



