Ɗan majalisar Amurka Riley Moore ya zargi gwamnatin Nijeriya da gazawa wajen kare Kiristoci duk da biliyoyin dalolin tallafin tsaro da take samu daga Amurka.
Jaridar Punch ta ruwaito Moore, wanda ke jagorantar kwamitin binciken da shugaban Amurka Donald Trump ya kafa kan zargin gallaza wa Kiristoci a Nijeriya, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a wani shiri na The Dinesh D’Souza a daren Alhamis.
Moore ya ce ‘yan’uwansa Kiristoci ana kashe su saboda imaninsu ga Yesu Almasihu, yana mai sukar shiru daga hukumomin Nijeriya da kuma kasashen duniya tare da gargadi cewa rashin daukar mataki kan matsalar na iya jawo tasirin tsaro mai muni.
Hakazalika, Moore ya bayyana halin da ake ciki a matsayin “kisan kiyashi da aka manta da shi”, inda ya bukaci Nijeriya da abokanta na waje da su dauki matakan gaggawa don kare rayukan Kiristoci da kawo karshen tashin hankali.



