Majalisar Wakilan Nijeriya ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa tawagar dan majalisa Jafaru Mohammed Ali, wanda ke wakiltar mazabar Borgu/Agwara ta Jihar Neja, a kan hanyar Lumma–Babanna a ranar Talata da yake kan hanyar taron mazabu.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun majalisar, Akin Rotimi, ya fitar a ranar Juma’a, harin ya yi sanadiyyar mutuwar wasu jami’an tsaro da ke rakiya tare da raunata direba da wasu daga cikin tawagar dan majalisar. Haka kuma an lalata wasu motoci a cikin tawagar.
Majalisar ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan jami’an da suka rasa rayukansu da kuma hukumomin tsaro, tare da rokon Allah ya ba wadanda suka ji rauni lafiya, tana mai kira da a gudanar da cikakken bincike domin kama wadanda suka aikata laifin.
Hakazalika, ta kuma jaddada cewa lamarin ya sake nuna gaggawar bukatar daukar mataki mai karfi da hadin gwiwa wajen yaki da matsalar rashin tsaro a yankunan kan iyaka, tare da alkawarin goyon bayan majalisa ga duk wani yunkuri na gwamnati wajen kawo karshen ta’addanci da garkuwa da mutane a fadin kasar.



