An shirya gudanar da babban taron tsaro a Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi, a ranar Litinin, 10 ga Nuwamba, 2025, domin tattauna hanyoyin magance karuwar matsalar tsaro a Arewacin Nijeriya.
Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III zai jagoranci taron tare da tsohon hafsan hafsoshin soji kuma tsohon ministan cikin gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau (rtd), tare da halartar gwamnonin Arewa, masana tsaro da sauran manyan jami’ai.
Shugaban kungiyar Arewa Broadcast Media Practitioners Forum, Alhaji Yelwa, ya ce taron zai samar da dandalin tattaunawa da hadin kai domin dawo da zaman lafiya da karfafa hadin kan kasa.
A cewarsa, taron zai hada ‘yan jarida, masu tsara manufofi, jami’an tsaro da kungiyoyin ci-gaba domin tsara dabarun sadarwa da za su taimaka wajen gina yardar jama’a, hana tsattsauran ra’ayi da tallafa wa gyaran tsarin tsaro na Nijeriya.



