Hukumar da ke kula da hana fataucin mutane, NAPTIP ta jihar Jigawa ta ce ta ceto mutane 221 da aka yi fataucinsu cikin shekaru biyu da suka gabata.
Kwamandan hukumar a jihar, Malam Abdulladir Turajo, ya bayyana hakan a taron wayar da kai da aka gudanar a Kazaure, inda ya ce an maido da waɗanda aka ceto zuwa ga iyalansu tun bayan kafa ofishin hukumar a watan Yuli 2023.
A cewarsa, hukumar ta samu hukunta masu laifina sau biyu tare da gudanar da shirye-shiryen wayar da kai guda 175 a makarantu, kasuwanni, wuraren ibada da tashoshin mota a fadin jihar.
Taron wanda aka shirya tare da ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Jigawa, na cikin shirin fadakarwa a matakin ƙananan hukumomi 27 na jihar, kuma an fara shi da yankin arewa maso yamma na jihar Jigawa.



