Dan takarar ADC a zaben gwamnan Anambra, John Nwosu, ya zargi jam’iyyar APGA da sayan da kuri’a a zaben da yake ci-gaba da gudana a jihar.
Nwosu ya bayyana hakan ne bayan ya kada kuri’arsa a Oduda Central School, Ward 2, da ke karamar hukumar Nnewi North ranar Asabar da misalin karfe 11:28 na safe, inda ya jaddada cewa ya gamsu da yadda jama’a suka fito, sai dai ya soki yadda ake raba kudi don jan hankalin masu kada kuri’a domin su zabi wata jam’iyya.
Kazalika, dan takarar jam’iyyar APC, Nicholas Ukachukwu, shi ma ya yi korafin cewa ana sayan kuri’a da tsoratar da wakilan jam’iyyu a wasu sassan jihar.



