Kungiyar Miyetti Allah reshen Jihar Benue ta roki gwamnatin Nijeriya da ta jiha da su shiga tsakani kan abin da ta bayyana a matsayin hare-hare da ake ta kaiwa ‘ya’yanta a karamar hukumar Ohimini a jihar Benue.
Shugaban kungiyar na jiha, Ardo Muhammad, wanda ya sa hannu kan wata sanarwa a ranar Juma’a, ya zargi al’ummar Awule tare da jami’an sa-kai na jihar da kai hare-hare kan sansanonin Fulani a yankin.
Muhammad ya bayyana cewa rikicin ya fara ne a karshen watan Agusta 2025 lokacin da wasu ‘yan bindiga daga al’ummar Awule tare da taimakon jami’an sa-kai suka kai hari kan sansanonin Fulani, inda suka kona sansanoni shida, suka kashe shanu 30, suka sace wasu, tare da kashe wani makiyayi mai suna Isu Abdulkarim.
A cewarsa, hare-haren sun ci-gaba a makonnin baya-bayan nan, abin da ya janyo asarar dabbobi da kuma raba makiyaya da muhallansu, yana mai musanta rahotannin da ke cewa makiyaya sun kai farmaki kan manoma.



