Shugaban ƙasar Djibouti mai shekaru 77, Ismail Omar Guelleh zai sake tsayawa takara karo na shida
Shugaban kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh, wanda yake mulki tun daga 1999, zai sake tsayawa takara a karo na shida a zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar a shekara mai zuwa, bayan majalisar dokokin ƙasar ta cire dokar da ke hana wanda ya haura shekara 75 tsayawa takara.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa shugaban majalisar dokokin kasar, Dileita Mohamed Dileita, ne ya tabbatar da hakan bayan taron jam’iyyar RPP, inda ya ce sun gama amincewa da Guelleh a matsayin ɗan takara.
Guelleh, mai shekaru 77, ya kasance cikin jerin tsoffin shugabannin Afirka da ke neman tsawaita mulkinsu, irin su Paul Biya mai shekara 92 na Kamaru, da Alassane Ouattara mai shekara 83 na Côte d’Ivoire.
A zaɓen shekarar 2021 ya samu nasara da kaso 97 cikin ɗari, yayin da jam’iyyarsa ke da rinjaye a majalisar dokokin kasar.



