DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Katsina ta musanta jita-jitar tashin hankali a wasan Katsina United da Barau FC

-

A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Katsina, Injiniya Sirajo Yazid Abukur, ma’aikatar ta bayyana cewa labarin da ake yadawa cewa magoya bayan Katsina United sun tayar da tarzoma a lokacin wasan su da Barau FC ba gaskiya ba ne.

Ma’aikatar ta ce bayan cikakken bincike daga jami’an tsaro, jami’an wasan, da masu sa ido masu zaman kansu, babu wani abu da ya nuna an samu tashin hankali ko jikkata mutum. An tabbatar cewa wasan ya gudana cikin kwanciyar hankali, inda magoya baya daga ɓangarorin biyu suka nuna ladabi da girmamawa.

Google search engine

Sanarwar ta yaba da yadda ’yan wasan da magoya bayan Katsina United ke ci gaba da zama abin koyi wajen nuna halin kirki a filayen wasa, tare da jaddada cewa Jihar Katsina ta dade tana da suna wajen nuna ɗabi’a da biyayya a wasanni.

Ta kuma shawarci jama’a da su guji yada labaran ƙarya da jita-jita marasa tushe da ka iya tayar da hankali, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da kula da harkokin wasanni cikin zaman lafiya da tsaro ga kowa da kowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara