Messi ya kafa sabon tarihi a duniyar kwallo bayan ya taimaka wajen cin kwallaye 400 a tarihinsa na kwallo wani abin da ba a taba yi ba.
Wannan nasara ta tabbata ne a wasan da Inter Miami ta lallasa Nashville SC da ci 4-0 a gasar Major League Soccer, kamar yadda mai rahoto kan harkokin wasanni Fabrizio Romano ya bayyana.
Messi ya taimaka wajen cin kwallaye biyu da Tadeo Allende ya zura a mintuna na 73 da 76.
A tsawon kusan shekaru 20 na aikinsa, Messi ya yi fice a kungiyoyin Barcelona, Paris Saint-Germain, da yanzu Inter Miami, inda ya ke ci gaba da kafa tarihi.



