Gwamnatin Nijeriya ta ce tana daukar matakai don inganta tsaro a duk fadin Nijeriya biyo bayan sabon gargadi game da tafiye-tafiye da Birtaniya ta fitar kan jihohi da dama sakamakon ta’azzarar ayyukan ta’addanci, sace mutane tare da yin garkuwa da su.
Ofishin harkokin waje na Birtaniya ya ja hankalin ‘yan kasarsa da su guji dukkan tafiye-tafiye zuwa jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Gombe, Katsina, da Zamfara, sannan ya yi gargadin kaucewa dukkan tafiye-tafiye sai dai idan ya zama dole.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya ce gwamnati ta san da matsalolin tsaro kuma tana aiki tukuru wajen magance su, da kara inganta kayan aiki da ayyukan leken asiri, haka kuma dukkan baki a Nijeriya za su kasance cikin tsaro yayin da matakan ke ci-gaba da aiki.
Sai dai gwamnatin Jihar Gombe ta musanta gargadin, tana mai cewa bayanan da Birtaniya ta fitar basu dace ba kuma babu adalci a cikin su.



