Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta yabawa shugaban Nijeriya Bola Tinubu bisa kare dimokuraɗiyyar Nijeriya ta hanyar guje wa tsoma baki a zaben gwamnan Anambra da aka gudanar a ranar Asabar.
Mai magana da yawun jam’iyyar a jihar, Mista Seye Oladejo, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce matsayar shugaban ta nuna jajircewarsa wajen tabbatar da sahihin zabe da kare dimokuraɗiyya.
Oladejo ya ce rashin tsoma bakin shugaban kasa a harkar zaben ya ƙara tabbatar da cancantarsa a matsayin gwarzon dimokuraɗiyya, tare da karfafa gwiwar jama’a a tsarin zabe.
Haka kuma, ya yabawa hukumar zabe ta INEC bisa gudanar da abin da ya kira zabe mai inganci da gaskiya, yana mai cewa jagorancin sabuwar hukumar ya kawo sabon salo na dimokuraɗiyya a Nijeriya.
A cewarsa, sakamakon zaben ya nuna rashin daidaito da tsari a cikin haɗakar jam’iyyun adawa, inda ya bayyana su a matsayin “taron ’yan siyasar da ke fafutuka da son zuciya ba tare da tsari ko hangen nesa ba.”



