Wata kotu a birnin Paris ta bayar da belin tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy a ranar Litinin, bayan da ya daukaka kara kan hukuncin da aka yanke masa bisa laifin hada baki wajen neman kudin kamfen daga tsohon shugaban Libiya, marigayi Muammar Gaddafi.
Sarkozy, wanda ya mulki Faransa daga 2007 zuwa 2012, ya fara zaman gidan yari ne a ranar 21 ga watan Oktoba bayan kotu ta same shi da laifin hada baki a watan Satumba, inda ya bayyana cewa zama a kurkuku ya kasance mawuyaci gare shi.
Kotu ta bayyana cewa Sarkozy ba barazanar guduwa yake ba, don haka zai fita daga gidan yari amma karkashin kulawar shari’a, ciki har da takaita tafiyarsa zuwa kasashen waje da kuma hana shi magana da jami’an ma’aikatar shari’a.
Dan karamin dansa Louis ya wallafa rubutu a shafinsa na X cewa, ” Taimakon Allah ga ‘yanci” tare da tsohon hotonsa da mahaifinsa bayan kotu ta amince da belin kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.



