Shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya (ASUU), Farfesa Chris Piwuna, ya ce gwamnatin kasar ba ta ɗauki harkar ilimi a matsayin abu mai muhimmanci ba, domin yawancin jami’an gwamnati ba sa kallon matsalolin fannin a matsayin lamari na ƙasa da ke buƙatar haɗin kai.
Yayin tattaunawar da aka yi da shi a shirin “The Toyin Falola Interviews” a ranar Lahadi, Piwuna ya bayyana cewa halin ko in kula na manyan jami’an gwamnati ne ke hana samun kyawawan sauye-sauye masu ɗorewa a fannin ilimi.
A cewarsa, mambobin majalisar zartarwa ta Nijeriya kan ɗauki matsalolin ilimi a matsayin aikin ministan ilimi kaɗai, ba abin da ya shafi sauran ma’aikatun gwamnati ba.
Piwuna ya ƙara da cewa rashin fahimta da cin hanci suna ƙara tsananta matsalar, yayin da ƙungiyar ASUU ke yin yajin aiki don neman a aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tun 2009 da kuma warware batutuwan da suka shafi albashi, tallafi da sabunta jami’o’in gwamnati.



