Wani mutum da ba a tantance bayanansa ba ya rasa ransa bayan ya yanke jiki ya fadi a wani gidan mata masu zaman kansu da ke titin Azikiwe, Mile 2 Diobu, a Fatakwal, Jihar Rivers a ranar Lahadi.
Wasu majiyoyi sun ce mutumin ya yi sa-in-sa da guda daga cikin ma’aikatan gidan kafin ya fadi kasa inda aka garzaya da shi asibiti, likitoci kuma suka tabbatar da mutuwarsa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa an mika binciken ga sashen binciken manyan laifuka (SCID).
Rundunar ta kuma tabbatar da kama wani mutum da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da wasu daga cikin matan da ke wurin suka arce bayan faruwar abin.



