Ministan Abuja Nyesom Wike, ya bai wa masu kadarori a Asokoro, Maitama, Garki da Wuse wa’adin ƙarshe na kwanaki 14 daga ranar 11 ga watan Nuwamba, 2025, don su bi dokokin amfani da ƙasa.
Mai taimaka wa ministan, Lere Olayinka, ya ce wa’adin ya biyo bayan ƙarewar wa’adin farko na kwanaki 30, inda ya gargadi masu kadarori cewa duk wanda bai bi doka ba za a ɗauki matakin karfi a kansa.
FCTA ta ce wuraren da abin ya shafa sun haɗa da Gana da Usuma a Maitama, Yakubu Gowon a Asokoro, da Aminu Kano da Adetokunbo Ademola a Wuse II inda aka umarci masu kadarorin da suka karya doka su biya tarar Naira miliyan biyar tare da sabunta takardunsu.
Wike ya kuma amince da sabbin takardun mallaka na shekaru 99 ga wadanda suka daidaita amfani da filaye, sai dai rangwamen bai shafi waɗanda aka riga aka soke filayensu ba.



