An samu musayar yawu a ranar Talata tsakanin ministan Abuja Nyesom Wike, da wani jami’in soja a yankin Gaduwa, Abuja, bayan takaddama kan iko da wani fili.
Bidiyon da aka gani ya nuna Wike yana zargin jami’in da mallakar filin ba bisa ka’ida ba, inda ya tambaye shi dalilin da ya sa sojoji ke iƙirarin mallakar filin a dalilin tsohon hafsan rundunar ruwan Nijeriya.
Jami’in, wanda ke sanye da kayan soji, ya ce an samu filin bisa doka kuma an bi dukkan ka’idojin da suka kamata, lamarin da ya fusata ministan har ya daka masa tsawa.
Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, rundunar sojin Nijeriya ko hukumar FCTA basu fitar da wata sanarwa ba.
Hukumar FCTA ta Abuja dai na ci-gaba da kokarin hana kwace filaye da gina gine-gine ba bisa ka’ida ba a fadin birnin.



