Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bukaci a kafa ‘yan sandan jihohi cikin gaggawa, yana mai cewa hakan ne kadai zai taimaka wajen kawo karshen matsalar tsaro a Nijeriya.
Uba Sani ya bayyana hakan ne a birnin Legas yayin wani taron da aka gudanar kan rawar da gwamnonin jihohi ke takawa domin yaki da matsalar tsaro.
Ya ce, rundunar tsaro irin su Amotekun a kudu maso yamma ba su da hurumin doka da zai ba su damar yaki da ‘yan ta’adda, saboda haka kafa ‘yan sandan jihohi ya zama wajibi idan har ana son kauda matsalar baki daya.
Gwamnan ya bayyana cewa Nijeriya na da ‘yan sanda kusan dubu 400 da kuma sojoji kasa da dubu 250, yayin da yawan jama’a ya haura miliyan 230.
Uba Sani ya kara da cewa gwamnatocin jihohi da sarakunan gargajiya ne suka fi sanin matsalolin tsaro a yankunansu, saboda haka dole a basu cikakken iko domin jagorantar wannan shirin na yaki da matsalar.



