Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar birnin Kano a matakin tarayya Injiniya Sagir Ibrahim Koki, ya bayyana ficewarsa daga NNPP saboda rikicin cikin gida da ke kara kamari a cikin jam’iyyar.
A cikin wata wasika da ya rubuta ranar 11 ga Nuwamba, 2025, wacce ya tura wa shugabar jam’iyyar na mazabar Zaitawa, Koki ya ce ya dauki wannan mataki ne bisa tsarin dokar ƙasa da ke ba kowane ɗan Nijeriya ‘yancin shiga ko barin kowace jam’iyya.
Ya ce rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar a matakin kasa ya yi tsananin da har ya zama abin da ke hana shi gudanar da aikinsa yadda ya kamata da kuma wakiltar al’ummar Kano Municipal yadda ya kamata.
Hon. Koki, wanda aka zabe shi karkashin jam’iyyar NNPP a 2023, ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta bashi ya yi hidima ga al’umma, yana mai bayyana cewa goyon baya da amincewar da ya samu daga ‘ya’yan jam’iyyar sun kasance abin alfahari.



