Majalisar wakilan Nijeriya ta katse zamanta na ranar Talata sakamakon zazzafar muhawara kan kasafin kudin 2026
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ba a samu gabatar da kuduri ko guda ba a zaman Talatar sakamakon daukar matakin, lamarin da ba a saba ganin irin sa ba.
Musayar yawu tsakanin ‘yan majalisar dai ya biyo bayan samun rabuwar kai game da yadda za a tafiyar da batun kasafin kudin Nijeriya na shekarar 2026.
Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga shugabancin majalisar, majiyoyi sun bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne kan wa’adin da aka bai wa ministocin kudi, kasafi da tsare-tsare tare da akanta janar na kasar, kan biyan basusukan da ‘yan kwangila ‘yan asalin Nijeriya ke bi.



