Gwamnatin Nijeriya ta ce tana kan hanyar ninka tattalin arzikinta bisa ma’aunin GDP zuwa shekara ta 2037, bisa hadin gwiwar da ke tsakanin ma’aikatar kudi da babban bankin Nijeriya (CBN).
Karamar ministar kudi, Doris Uzoka-Anite ce ta bayyana haka a ranar Talata a Abuja yayin da take gabatar da jawabi a taron shekara-shekara na manyan jami’an babban bankin Nijeriya.
Ta ce samun hadin kai tsakanin bangarorin da suka shafi kudi na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasar.
A cewarta, burin gwamnati shi ne ta cimma karuwar GDP sama da kashi 4% a kowace shekara zuwa 2027, wanda hakan zai ninka darajar tattalin arzikin Nijeriya zuwa 2037 idan aka ci gaba da samun karuwar da ta kai kashi 7% a duk shekara.



