Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya jinjina wa maza da mata na rundunar sojojin Nijeriya bisa jajircewa da sadaukarwar da suke yi don kare ƙasar daga barazanar tsaro.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Tinubu ya bayyana hakan ne a taron ƙungiyar Editocin Nijeriya NGE da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba, inda ya ce sojojin suna fuskantar haɗari domin kare mutuncin kasar.
Shugaban ya ce duk da ƙalubalen da ake fuskanta na ta’addanci da ‘yan bindiga, gwamnatinsa tana ɗaukar matakai don karfafa rundunar sojoji da sauran jami’an tsaro.
A cewar sa, ya zama wajibi a ci gaba da kare su da kuma ba su goyon baya duba da irin hadarin da suke fuskanta.



