Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kudu maso gabashin Nijeriya Ijeoma Arodiogbu, ya ce rade-radin da ake yi cewa Atiku Abubakar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin yin kawance kafin zaben 2027 ba shi da tushe ballantana makama.
Jaridar Punch ta rawaito Arodiogbu na cewa babu wata hanya da tsohon gwamnan na Kano zai koma tafiya ɗaya da Atiku, duk da kyakkyawar mu’amalar da suka nuna a bikin zagayowar ranar haihuwar Kwankwaso makonni biyu da suka gabata.
Ya ce idan Kwankwaso zai yi wani sauyi, zai fi dacewa ya koma APC domin hakan zai fi amfani a siyasarsa, ya ce ko da Atiku ya yi yunƙurin bai wa Kwankwaso wata dama hakan ba zai yi wani tasiri ba.



