Jam’iyyun hamayya na NNPP da ADC reshen jihar Osun sun ce halin tsananin talauci da ake ciki yanzu shi ne zai yanke wa shugaban Nijeriya Bola Tinubu hukunci a zaben 2027, ba wai sauye sauyen jam’iyya ko dabarun siyasa ba.
Jaridar Punch, ta ruwaito cewa jam’iyyun biyu sun bayyana haka ne sakamakon yawaitar sauya sheka da ke faruwa a PDP, LP da NNPP, ciki har da gwamnoni uku da suka bar PDP a cikin watanni biyu da suka wuce domin komawa APC.
Mai magana da yawun NNPP, Dipo Johnson, ya ce duk da barin wasu ‘yan majalisa, jam’iyyar tana rike da mafi yawa daga cikin wakilanta 19, yana mai zargin APC da amfani da kudi wajen ingiza ‘yan majalisun tarayya zuwa jam’iyyarsu.



