Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya nesanta kansa daga matakin jam’iyyar PDP na korar Ministan Abuja, Nyesom Wike, da tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, da sauran manyan jiga-jigai da aka zarga da yi wa jam’iyyar zagon kasa.
A cikin wata sanarwa da daraktan yada Labaran gwamnan Gyang Bere ya fitar, Mutfwang ya bayyana cewa wannan batu ba a tattauna shi ba a taron Gwamnonin PDP kafin a gabatar da shi a gangamin jam’iyyar da ake gudanarwa a Ibadan.
Ya ce matakin da aka dauka bai dace ba, kuma ba shi ne hanya mafi dacewa don magance rikicin jam’iyyar ba.



