Shugaban jam’iyyar NNPP na Nijeriya Ajuji Ahmed, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta sake lashe zaben jihar Kano a 2027 duk da ficewar wasu ’yan majalisa daga cikinta.
Jaridar Punch ta rawaito Ajuji na cewa, rahotannin ficewar wasu mambobin majalisar wakilai daga jam’iyyar zuwa APC ba su rage damar da NNPP ke da shi ba, domin ficewar ta su jawo sababbin mambobi da dama suna shiga jam’iyyar musamman daga Kano.
Ficewar Abdulmumin Jibrin Kofa da Sagir Koki zuwa APC a ranar Alhamis ta biyo bayan karanta wasikunsu da kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas ya yi, inda suka zargi rikicin cikin gida na jam’iyyar NNPP a Kano a matsayin dalilin ficewar.
Sai dai Ahmed ya ce NNPP ba ta damu ba, domin suna samun sababbin mambobi masu yawa, yana mai bayar da tabbatacin cewa NNPP za ta ci gaba da rike Kano.



