DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kasashen Nijeriya, Mozambique da Sudan na daga cikin kasashen da ake musguna ma Kiristoci – Shugaban darikar Katolika

-

Jagoran Katolika, Pope Leo XIV, ya saka Najeriya cikin jerin kasashen da Kiristoci ke fuskantar tsangwama, tare da Bangladesh, Sudan, Mozambique, da wasu ƙasashe.

Leo ya wallafa hakan ne a shafinsa na X, inda ya nuna damuwarsa kan hare-haren da ake kaiwa al’ummomin Kiristoci da coci-coci, sannan ya yi kira da yin addu’o’i don zaman lafiya da hadin kai.

Google search engine

Maganganun Pope sun yi daidai da na shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya sanya Nijeriya a matsayin ‘kasar da ke cikin damuwa ta musamman’ kan tsangwamar addini ga Kiristoci wanda hakan ya jawo hankalin duniya kan batun tsangwamar addini a Nijeriya.

Sai dai gwamnatin Nijeriya ta musanta wannan zargi, tana mai cewa kasar ba ta nuna wariya ga wani addini ba, kuma tana matsayin kasa mai zaman lafiya da bin doka. Gwamnatin ta jaddada cewa matsalolin tsaro da ake fuskanta ba na addini ba ne, sai dai na laifuka daban-daban.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Atiku Abubakar ya nuna damuwarsa kan sace dalibai a jihar Kebbi

Madugun adawa a Nijeriya, Atiku Abubakar ya bayyana damuwa kan harin da aka kai Makarantar ‘yan mata ta Gwamnati da ke Maga a Jihar Kebbi,...

Jami’an tsaro sun kaddamar da shirin ceto daliban da aka sace a jihar Kebbi

’Yan sanda da sojoji sun kaddamar da bincike da aikin ceto domin kubutar da dalibai 25 da aka sace daga makarantar ’Yan Mata ta gwamnati...

Mafi Shahara