Kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta yi tir da zanga-zangar da wasu ‘yan APC na jihar Filato suka yi a Jos domin nuna kin amincewa da yiwuwar gwamna Caleb Mutfwang ya koma jam’iyyar inda ta bayyana wannan mataki a matsayin ba na dimokuradiyya ba ne, kuma babu wata doka da ta halatta shi.
A cewar shugaban kungiyar, Alhaji Saleh Zazzaga, babu wani mutum ko rukuni da ke da ikon hana kowane ɗan Najeriya shiga jam’iyyar da yake so, ciki har da gwamna mai mulki.
Zanga-zangar dai ta faru ne a yayin tarbar sababbin ‘yan jam’iyya da aka yi, inda wasu suka daga alluna suna nuna adawa da shigowar Mutfwang kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Kungiyar ta sake jaddada kiran da take yi wa Mutfwang ya sauya sheƙa zuwa APC domin ƙara wa jam’iyyar ƙarfi kafin 2027, tana zargin masu adawa da yunkurin da neman biyan bukatunsu na kai.
Punch ta ruwaito cewa kungiyar ta nemi Shugaba Bola Tinubu da tsohon gwamna Simon Lalong su shiga tsakani domin tabbatar da cewa an karɓi gwamnan cikin sauƙi.



