Matatar man Dangote ta bayyana rahotannin da ke cewa saukin farashin fetur ya samo asali ne daga dakatar da harajin shigo da fetur da dizal na kashi 15 a matsayin shaci-fadi.
Kamfanin ya ce gaskiyar lamarin shi ne saukin ya samo asali ne daga rage farashin wasu kayayyaki da kashi 5.6 a ranar 6 ga Nuwamba.
Dangote ya jaddada cewa harajin kaso 15 na shigo da kaya ya riga ya samu amincewar shugaban Nijeriya tun ranar 21 ga watan Oktoba, kuma hakan bai yi tasiri kan farashin kamfanin ba.
Hakazalika, ya tabbatar da ci-gaba da samar da fetur mai inganci a farashi mai rahusa, tare da kira ga kafofin watsa labarai da masu ruwa da tsaki su dogara kan sahihan bayanai wajen sanar da jama’a.



