Shahararriyar mawakiyar Amurka, Onika Maraj-Petty wadda aka fi sani da Nicki Minaj, za ta yi jawabi gaban Majalisar Dinkin Duniya a New York a ranar Talata, inda ake sa ran za ta tabo batun hare-haren da ake cewa ana kai wa Kiristoci a Nijeriya.
Za ta bayyana ne tare da jakadan Amurka a MDD, Michael Waltz, da Alex Bruesewitz, ma ba shugaban Amurka Donald Trump shawara.
Wannan ci-gaban ya fito ne daga rahoton Eric Cortellessa na mujallar Time, wanda ya tabbatar da halartar Minaj inda Waltz ya yabe ta, yana cewa ba wai ta shahara a kiɗa kaɗai ba, har ma tana da jajircewar magana kan abin da take ganin rashin adalci ne, musamman abin da ya kira cin zarafi ga Kiristoci a Nijeriya.
Minaj ta mayar da martani tana godiya saboda gayyatar, tare da cewa ba za ta yi shiru ba kan duk wani abu da ta dauka a matsayin rashin adalci kuma wannan wani hakki ne da take dauka da muhimmanci.
Shirye-shiryen taron sun biyo bayan ikirarin Trump na cewa ana aiwatar da kisan kiyashi ga Kiristoci a Nijeriya, yana mai kira ga Majalisa ta dauki mataki gaggawa.
Sai dai gwamnatin tarayya ta musanta wannan zargi, tana cewa matsalar tsaron Nijeriya ba ta ta’allaka ba da addini, duk da cewa jami’an Amurka na ci-gaba da nuna damuwa.



