Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya gargadi alkalan Najeriya cewa dole adalci ya kasance a tsarkake ba tare da yunƙurin cakuda shi da rashawa ba.
Yayin taron alkalai da aka buɗe a Abuja a ranar Litinin, Tinubu ya ce alkalan manyan kotuna su ne ginshikan adalci, kuma gwamnati za ta ci gaba da zuba jari a horo, jin daɗi da aikin cibiyar shari’a ta ƙasa.
Tinubu ya jaddada cewa babu wani gyara da za ya yi tasiri ba tare da gaskiya da rikon amana ba, yana gargadin cewa cin hanci a bangaren shari’a na iya rushe ƙasar baki ɗaya.
Ya kuma nuna damuwa kan yawan shari’o’in da ke taruwa da jinkirin yanke hukunci, yana mai cewa dole kotuna su ɗauki matakai na gaggawa domin dawo da amincewar jama’a da ƙarfafa tsarin mulkin Nijeriya.



