Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, Super Eagles bisa jajircewarsu a wasan neman gurbin gasar cin kofin duniya ta 2026, duk da rashin nasarar da suka sha a hannun DR Congo bayan bugun fenariti a Rabat, Morocco.
Wasan ya ƙare 1 da 1 bayan mintuna 120, inda DR Congo ta doke Nijeriya da ci 4 da 3 a bugun fenariti.
Tinubu ya ce dole a jinjina ƙoƙarin ‘yan wasan duk da ba a samu sakamakon da ake so ba, kamar yadda mai ba shi shawara kan labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a duba kura-kuran da aka samu a wasan, tare da gyara duk wani gibin da ya hana ƙungiyar samun nasara.
A cewarsa, yanzu hankali ya koma kan gasar kofin nahiyar Afrika da za a yi a Morocco daga watan Janairu zuwa Fabrairu 2026 inda ya ce Super Eagles na bukatar dawo da kima da martabarsu a gasar nahiyar.
Tinubu ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya su cigaba da mara wa ƙungiyar baya, yana cewa duk da rashin sa’a, Eagles sun nuna jajircewa da himma tun daga wasan farko har zuwa bugun fenaritin da ya yanke hukuncin karawar.



