Rundunar ’yan sandan Abuja ta musanta rahotannin da ke cewa an yi yunkurin hallaka jami’in sojan ruwa, Laftanar Ahmed Yerima, a Abuja inda ta ce labarin ba gaskiya ba ne kuma ba a samu rahotonsa a ko’ina cikin birnin ba.
Rahotannin da suka bazu a kafofin sada zumunta sun yi zargin cewa wasu da ba a san ko su wanene ba, sanye da kata bakake, a cikin motocin Hilux marasa lamba, sun bi motar Yerima daga NIPCO a Kubwa zuwa hanyar Gado Nasco.
Wasu sun alakanta lamarin da sabanin filin da ya shiga tsakaninsa da Ministan FCT, Barista Nyesom Wike kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar, ta ce babu wani rahoto da aka samu game da haka, kuma jama’a su yi watsi da labarin domin kauce wa tada hankula.
Rundunar ta kuma gargadi jama’a da su guji yada bayanan da ba a tabbatar da su ba domin kauce wa haifar da firgici ba gaira ba dalili.



