Babban hafsan rundunar sojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya umarci dakarun Operation Fansan Yamma da su matsa kaimi wajen ceto daliban GGCSS Maga da aka yi garkuwa da su a Danko/Wasagu.
A cikin wata sanarwa da Kyaftin David Adewusi ta bayyana, Janar Shaibu ya umurci haka ne yayin kai ziyarar aiki a jihar Kebbi inda ya bukaci dakarun su yi aiki bisa bayanan leƙen asiri tare da bin sawun ’yan bindiga dare da rana, sannan da hada kai da ’yan banga da mafarauta domin sanin hanyoyin yankin.
Haka kuma, ya kai ziyarar ta’aziyya ga sarkin Danko da shugabar makarantar, yana tabbatar musu da cewa rundunar soji za ta tabbatar an kubutar da daliban ba tare da lahani ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa, ya umarci dakaru su kasance masu ladabi da ƙwarewa tare da bin ka’idojin aiki domin dawo da zaman lafiya a Kebbi da yankunan da ke makwabtaka.



